Marghi
Marghi | |
---|---|
| |
Lamban rijistar harshe | |
ISO 639-3 |
mrt |
Glottolog |
marg1265 [1] |
Harshen Marghi ko Margi, Harshen Marghi yare ne dake da asali a kasar Nijeriya, Kameru da kuma Cadi da wasu bangaren kasashe kamar Nijar, da Sudan. kuma akwai masu amfani da harshen ako'ina a cikin kasashe daban-daban dake a fadin duniya, amma mafiya yawan masu amfani da harshen suna zaune ne a jihohin Nijeriya da suka hada da Borno, Adamawa, Yobe da sauran kasashen dake makota da jihar Borno kamar irin su Kamaru, chadi da Nijar.
Mutanen Marghi mutane ne wadanda mafiya yawansu manoma ne da kiwo kuma suna zama ne tare da Kanuri, Fulani da dai sauransu. Sannan suna da kyakkyawar alaka da dangantaka musammam ma da fulani na aurataiya, taimakon juna, kasuwanci, barkwanci da kyakkyawar fahimtan juna. Marghi mutane ne masu son zaman lafiya da girmama mutane ga karamci. Marghi mutane ne da aka sani wajen dagiya da juriya ga jajircewa game da dukkan sha'ani na rayuwa kamar neman ilimi, neman halas, kokarin kawo cigaba akan komai. Mutane dayawa suna bada musali da Margunawa cewa, matukar akwai margi a waje to ba'a fushi saboda iya barkwancii da kwantar wa mutane da hankali.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Hammarström, Harald; Forkel, Robert; Haspelmath, Martin, eds. (2017). "Marghi". Glottolog 3.0. Jena, Germany: Max Planck Institute for the Science of Human History.